Jiya Asabar ranar 30 ga watan Satumba, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya gana da kwararrun kasashen waje da iyalansu, wadanda suka samu lambar yabo ta Sada Zumunta ta shekarar 2017 da gwamnatin kasar Sin ta bayar.
Yayin ganawar, firaminitan ya taya su murnar samun lambar yabon, kuma ya nuna amincewa sosai ga kokarinsu na sa kaimi ga ci gaban kasar Sin musamman ma na yankunan da ke tsakiya da yammacin kasar, gami da sada zumunci a tsakanin Sin da ketare.
Haka kuma Li Keqiang ya yi fatan cewa, kwararru da masana na kasashen waje za su kara bada gudummawarsu ga aikin zamanintar da Sin, da kyautata fasahohin zamani, domin ba da taimako ga aikin canja salon tattalin arzikin kasar Sin, ta yadda za a iya sa kaimi ga farfadowar tattalin arzikin duniya baki daya.(Kande Gao)