in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'in shirin nukiya na MDD yace Iran na aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma game da nukilya
2017-10-30 10:45:20 cri
Babban jami'in dake sa ido kan shirin makaman nukiliya na MDD (IAEA) ya jaddada cewa, Iran tana aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma da ita karkashin yarjejeniyar shekarar 2015.

Hukumar (IAEA) ta sanar cewa, babban daraktanta Yukiya Amano, ya gana da shugaban kasar Iran Hassan Rouhani, da mataimakin shugaban kasar kuma babban jami'in kula da shirin nukiliya na kasar Ali Akbar Salehi, da ministan harkokin wajen kasar Mohammad Javad Zarif, a lokacin da ya ziyarci Tehran babban birnin kasar.

Tun a watan Janairun shekarar 2016, hukumar IAEA tana ta tantancewa da kuma sa ido game da yadda Iran ke cika alkawuranta da suka shafi nukiliya karkashin wani cikakken shiri na (JCPOA), wanda kwamitin tsaron MDD ya amince da shi a shekarar 2015.

Amincewar mambobin kasashe 5 masu kujerun dindindin a MDD, da kuma kasar Jamus, da kungiyar tarayyar turai (EU), da ita kanta kasar Iran, ya bada damar daukar matakai game da sanya ido kan shirin nukiliyar Iran, kuma hakan ya bada damar duba yiwuwar dage takunkumin da MDD ta kakabawa kasar.Sanarwar tace, tantancewa da kuma sanya idon na hukumar IAEA, an gudanar da shi ne bisa gaskiya da adalci, kuma karkashin shirin JCPOA da kuma cikakken tsarin kiyaye ka'idoji.

A ranar Lahadi shugaban kasar Iran Rouhani, ya bukaci babban jami'in shirin nukilya na MDD ya bada tabbaci game da irin biyayyar da kasarsa ta yi dangane da yarjejeniyar kwance shirin nukilyar data kulla da manyan kasashen duniya masu karfin fada a ji bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya ki akincewa da tabbatar da wannan yarjejeniya.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China