Jaridar Tehran Times ta kasar Iran ta ruwaito, Bageri ya bayyana hakan ne, yayin da ya halarci wani taron dakarun soja a wannan rana cewa, yana mai cewa dalilin daddale yarjejeniyar batun nukiliyar kasar Iran shi ne a soke takunkumin da kasashen yammacin duniya suka sakawa kasar ta Iran. Don haka idan har aka mayar da takunkumin, ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar ba shi da wata sauran ma'ana.
Bageri ya jaddada cewa, kasar Iran ta yi alkawarin bin yarjejeniyar batun nukiliya ta, amma idan kasar Amurka ta sake saka mata takunkumi, Iran din za ta janye daga yarjejeniyar. (Zainab)