A wata sanarwar data fitar, majalsiaar kolin kasar Rashar ta bukaci mambobin majalisar dokokin Amurka dasu gaggauta yin duk abin da ya dace domin shawo kan duk wata matsala da ka iya jefa batun cikin matsanancin hali.
Majalisar ta kuma bukaci majalisun dokokin kasashen Jamus, Faransa, China, Birtaniya da kungiyar tarayyar Turai, da su yi amfani da dukkan matsayin da suke da shi ta hanyar daukar matakan siyasa domin ganin an kiyaye yarjejeniyar da aka cimma mai cike da tarihi.(Ahmad Fagam)