Kamfanin dillancin labaru na kasar Iran ya ruwaito Ali Akbar Salehi na bayyanawa 'yan jarida cewa, a matsayinta na kasar da ta sa hannu kan yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya, Iran ta daddale yarjejeniyar kan karin wasu batutuwa don cimma burin hana yaduwar makaman, sai dai majalisar dokokin kasar ba ta kai ga zartar da ita ba, a don haka ya ce ba ta da wani amfani.
Ya ce idan aka soke yarjejeniyar nukiliya kasar, to babu bukatar ta ci gaba da aiwatar da waccan yarjejeniyar kan karin batutuwa.
Har ila yau, ya ce, idan Iran ta lura cewa, yarjejeniyar nukiliyar ba ta amfana mata, to za ta dawo da aikin tace sinadarin Uranium da kashi 20 cikin dari, a cewarsa kasar za ta dawo da aikin cikin kwanaki hudu.
Ali Salehi ya kuma zargi shugaban kasar Amurka Donald Trump da nuna kiyayya ga Iran da kin bincike kan sansanin sojan kasar. (Zainab)