Mr. Wang ya ce Sin ita ce kasa ta 2 mafi karfin tattalin arziki, kana yawan kudaden da kasuwar ta gida ka iya bukata nan da shekaru 5 masu zuwa, za su kai dalar Amurka tiriliyon 10. Kaza lika za ta ci gaba da samun bunkasar tattalin arziki na kaso 6.5 bisa dari.
Jami'in ya kara da cewa, karin sassa da a baya ake dari dari da su, za a bude su ga masu zuba jari daga ketare, yayin da ake kara samar dokoki da saukaka matakai, na gudanar da hada hadar kasuwanci ga masu zuba jari a cikin kasar. (Saminu Hassan)