Wata majiyar soja ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, an shafe sama da mako guda ana gwabza fada tsakanin kungiyoyin 'yan tawaye masu dauke da makamai dake gaba da juna da sojojin gwamnati, a wani mataki na kakkabe munanan laifuffuka a yankin, lamarin da ya kai ga kisa tare da jikkata mayakan da yawansu ya kai 40, yayin da sojojin gwamnati 4 suka mutu kana wasu 10 kuma suka ji rauni.
Majiyar ta kara da cewa, tun a ranar Larabar da ta gabata ce, sojojin gwamnati suka kwace sansanin soja mafi girma dake yankin Warshaffana.
Ofishin hulda da jama'a na sojojin ya sanar da cewa, kwamandan sojojin dake gabashin kasar, janar Khalifa Haftar, ya gana da kwamandojin soja dake yankin na Warshaffana, jim kadan bayan da sojojin gwamnatin suka sanar da kwace iko da yankin baki daya. (Ibrahim Yaya)