Peter Millet ya sanar da haka ne a jiya, lokacin da yake ganawa da Fayez Serraj, firaministan gwamnatin Libya da MDD ke marawa baya.
A cewar ofishin yada labarai na Firaministan, Peter Millet ya ce nan bada dadewa ba, za a bude ofishin jakadancin Birtaniya a Tripoli, shekaru 3 bayan rufe shi bisa tabarbarewar tsaro a kasar.
Jami'an biyu sun kuma tattauna kan hadin giwar dake tsakani Birtaniya da Libya, tare da yanayin da tsaron Libya ke ciki a baya-bayan nan.
Fayez Serraj ya kuma sabunta kira ga kasashen duniya su gaggauta gudanar da cikakken bincike kan hari ta sama da wani jirgin da ba a san inda ya fito ba, ya kai birnin Derna dake gabashin kasar a kwanakin baya, al'amarin da ya yi sanadin gomman rayuka, ciki har da fararen hula. (Fa'iza Mustapha)