in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin ruwan Libya sun ceto bakin haure 200 a tekun kasar
2017-11-05 13:24:41 cri
Sojojin ruwan kasar Libya sun yi nasarar ceto bakin haure ta haramtattun hanyoyi kimanin 200 a ranar Asabar.

Wani jami'in sojin ruwan kasar Mahmoud Shabrak, ya shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, dakarun sojin ruwan Libya masu aikin sintiri sun yi nasarar ceto bakin hauren 200 wadanda ke cikin wani kwale kwale na roba wanda ya yi hadari a ruwan tekun Libyan.

A cewar Shabrak, wadanda aka ceto din sun hada da mata wadan da 'yan kasashen Afrika ne.

Bakin hauren da sojin ruwan na Libya suka ceto an killacesu a wata cibiya, sai dai suna cikin hali matsin rayuwa.

Kasar Libya ta kasance tamkar wata matattarar da bakin haure ta barauniyar hanya ke amfani da ita wajen tsallaka ta tekun Mediterranean zuwa nahiyar Turai, sakamakon rashin tsaro da oda a kasar ta Libya, tun bayan kifar da gwamnatin shugaba Muammar Gaddaf a shekarar 2011. Sai dai da dama daga cikin bakin hauren sun nitse har sun mutu a kan hanyar.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China