Dakarun sojin sun kame helkwatar ta Faraj Eg'em ne dake gundumar Budzira, kuma sun karbe ikon helkwatar baki daya, tare kuma da kwace dukkan motocin dake wajen, sai dai ba'a samu harasarar rayuka ko dukiya ba a lokaicin faruwar lamarin kamar yadda hukumar sojin ta shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua.
A makon jiya ne dai wani harin bom cikin wata mota ya tarwatsa tawagar dake yiwa Eg'em rakiya a Benghazi, lamarin da ya haddasa mutuwar wani jami'in tsaro guda, kana wasu mutanen 4 suka jikkata.
A watan Augasta ne gwamnatin hadin kan kasa dake birnin Tripoli ta nada Faraj Eg'em a wannan mukamin. Matakin da ya harzuka janar Khalifa Haftar, inda ya gabatar da wata doka dake haramtawa duk wani jami'in gwamnati zartar da wani hukunci a yankunan kasar dake karkashin ikon sojoji. (Ahmad Fagam)