in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a jibge wani rukunin sojojin Nijar na hudu a arewacin Mali
2016-08-03 10:14:32 cri
Wani rukunin dake kunshe da sojojin Nijar 850 zai isa a arewacin Mali nan da 'yan kwanaki masu zuwa bisa tsarin tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD dake kasar Mali (MINUSMA), in ji wata majiyar tsaro a ranar Talata a birnin Niamey. Rukunin farko dake kunshe da kayayyaki kawai ya bar Niamey a ranar Talata kana sauran rukunin zai tashi ba da jimawa ba, a cewar wannan majiya. Rukunin sojojin Nijar na hudu na MINUSMA zai shafe tsawon shekara guda a Mali.

Sojoji 850 sun samu horo sosai na tsawon makwanni goma a birnin Ouallam, mai tazarar kilomita 100 daga arewacin Niamey, game da ayyukan wanzar da zaman lafiya kamar da dokokin MDD suka tanada. Za'a jibge su a arewa da kuma arewa maso gabashin Mali a kan iyakar kasashen biyu, wani yankin dake fama da ayyukan 'yan ta'adda dake neman tada zaune tsaye a Nijar da Mali, a cewar shugaban rundunar sojojin Nijar, Janar Seyni Garba.

A cikin watan Janairun shekarar 2013, rukunin sojojin Nijar na farko dake kunshe da sojoji 680 ko fiye, an jibge su bisa tsarin tawagar kasa da kasa ta ba da goyon baya ga kasar Mali (MISMA), domin yaki da kungiyoyin 'yan ta'adda da suka mamaye arewacin Mali, tare da kwato dukkan fadin kasar Mali.

Nijar da Mali na raba kan iyaka guda bisa tsawon kilomita fiye da 800, haka al'ummomin dake ga bangaren biyu na magana da harsuna guda kamar Tamajek (Buzanci), Songhoi (Zabarmanci), da Fulfulde wato fulatanci. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China