Rear Admiral Joseph Okojie, shi ne kwamandan rundunar tsaron hadin gwiwa a yankin Niger Delta, ya shedawa manema labaru a birnin Yenagoa cewa, jami'an sojojin da aka tura a ranar Litinin zuwa yankin Kaima a jahar Bayelsa, na daya daga cikin matakan tabbatar da zaman lafiya a yankin.
An tura dakarun sojoji tare da kayayyakin aiki zuwa yankin na Kaima a jahar Bayelsa ne, sakamakon barazanar da tsagerun yankin Niger Delta ke yi na yunkurin karbe iko a yankin.
A watanni uku da suka shude, tsagerun yankin sun haifar da koma baya ga cigaban tattalin arzikin Najeriya, sakamakon kaddamar da hare hare, tare da lalata bututun danyen mai da iskar gas a yankin .(Ahmad Fagam)