in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya ta sanar da saukaka matakan bada takardun visa ga masu zuba jari a kasar
2017-03-24 10:05:02 cri
Hukumomin a Najeriya sun sanar da aniyar gwamnatin kasar ta samar da takardun izinin shiga kasar bayan an isa wato visa-on-arrival ta intanet ga masu zuba jari a matsayin wani mataki da zai taimaka wajen bude kofa ga masu son zuba jari a kasar.

Kwantirola janar na hukumar shigi da fici ta Najeriyar Muhammad Babandede, yace bullo da sabon tsarin neman takardun visar ya biyo bayan sauye sauyen da aka samu ne game da yadda duniya ke tafiyar da wannan fanni a halin yanzu, kuma hakan na daga cikin matakan da zasu janyo hankulan masu sha'awar zuba jari daga kasashen ketare a Najeriyar, kana matakin zai kara samar da kwararru ga kasar ta yammacin Afrika.

Da yake sanar da wannan mataki a birnin Abuja Babandede, yace wannan matakin zai biya muradun masu neman takardun na visa daga ko ina a duniya tun daga lokacin da suka gabatar da bukatar ta yanar gizo cikin sa' o'i 48.

Wannan sabon mataki na daga cikin kudurorin da majalisar habaka cigaban kasuwanci ta kasar ta amince da shi da zummar samar da kyakkyawan yanayin kasuwanci ga 'yan kasashen waje dake sha'awar zuba jari a kasar, in ji jami'in.

Yace sabon matakin zai magance wahalhalun da ake fama dasu a tsohon tsarin neman takardun visar da ake amfani da shi a baya.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China