Hafsan sojin wato birgadiya janar Victor Ezugwu, ya ce, da ma an kama wadannan mutane a yayin da sojoji suke gudanar da ayyukansu daban daban na murkushe 'yan ta'adda a jihar Borno. Cikin mutanen, akwai maza 114, da mata 107, gami da yara 127, a cewar hafsan.
Ezugwu ya kara da cewa an riga an mika mutanen ga Kashim Shettima, gwamnan jihar Borno, yayin wani bikin da aka gudanar da Maiduguri, hedkwatar jihar. Kafin hakan, a cewar hafsan, an yi wa mutanen tambayoyi don tabbatar da cewa ba su da wata alaka da kungiyar Boko Haram.
Kuma daga karshe an tabbatar da cewa wadannan mutane ba su da wani laifi, shi ya sa aka yanke shawarar sakin su nan take, domin su koma zaman rayuwarsu yadda ya kamata bisa 'yanci da dokokin kasa.(Bello Wang)