in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masar ta cancanci shiga gasar kwallon kafa ta duniya ta 2018 bayan ta doke Congo da ci 2 da 1
2017-10-09 09:49:12 cri
Bayan shafe shekaru sama da 20 ba'a ji duriyarta ba, babbar kungiyar wasan kwallon kafa ta kasar Masar ta samu nasarar shiga gasar cin kofin duniya wanda za'a gudanar a kasar Rasha a shekara mai zuwa, bayan da ta samu galaba akan takwararta kungiyar wasan kwallon kafa ta Jamhuriyar Congo, inda aka tashi da ci biyu da daya a wasan da aka buga a filin wasan kasar Masar dake birnin Alexandria.

Masar ta kasance kasa ta biyu daga nahiyar Afrika da ta samu nasarar shiga gasar bayan Najeriya, inda ta samu gurbi a jadawalin hukumar FIFA a wasan da za'a gudanar a kasar Rasha, wannan nasara da Masar ta samu ta kasance abin da kasar ta jima tana burinsa inda za ta halarci gasar kwallon kafa ta duniya a karo na uku bayan makamancinsa a shekarar 1990 da kuma 1934.

Shahararren dan wasan gaba na kasar Masar Mohamed Salah, wanda a halin yanzu yake taka leda da kungiyar wasan kwallon kafa ta Liverpool, shi ne ya zarawa Masar kwallaye biyu bayan fara wasan da mintoci 63 da kuma mintoci 93.

Nasarar da Masar ta samu ta shiga gasar kwallon kafa ta duniya ta 2018 ta kawo karshen burin da abokan hamayyarta na kasashen Afrika a rukunin na 5 ke da shi, wadanda suka hada da kasashen Uganda, Ghana da Jamhuriyar Congo.

Bayan nasarar da kungiyar wasan ta samu, shugaban kasar Masar Abdel-Fattah al-Sisi ya amince da bayar da kyautar fam miliyan 1.5 na kudin kasar, kwatankwacin dalar Amurka dubu 85 ga kowanne dan wasa saboda nasarar da suka samu, al-Sisi ya ce sun nuna kyakkyawan misali na tsayawa tsayin daka da kuma yin aiki tukuru. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China