Al'ummar Masar sun cika da murna bisa nasarar da Kungiyar kwallon kafar kasar ta yi na samun cancantar shiga gasar cin kofin duniya ta 2018
An shafe tsawon dare ana murna a Masar, biyo bayan nasarar da kungiyar kwallon kafar kasar ta yi, na samun gurbin buga wasa a gasar cin kofin duniya ta 2018 da za a yi badi a Rasha, bayan ta doke takwararta ta kasar Congo da ci 2-1 a wasan da suka buga da yammacin jiya Lahadi a filin wasa dake birnin Alexandria.
Tun kafin karfe 12 na dare, dubban mutane suka yi dandazo a wajen filin wasan Borg El Arab, inda suka yi ta murna suna daga tutocin kasar tare da danna ham na motocinsu duk cikin murnar nasarar da kasar ta samu na cimma burinta na shiga gasar cin kofin duniya bayan ta shafe shekaru 27 tana jira. (Fa'iza Mustapha)