in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya halarci kwarya-kwaryan taron shugabannin kasashe membobin kungiyar APEC karo na 25
2017-11-12 13:28:42 cri

An gudanar da kwarya-kwaryan taron shugabannin kasashe membobin kungiyar APEC karo na 25 a birnin Da Nang dake kasar Vietnam a jiya Asabar, inda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron, kana ya gabatar da jawabi mai taken "yin kokari tare don bude sabon babi na hadin gwiwar dake tsakanin kasashen Asiya da yankin tekun Pasifik", inda ya jaddada cewa, kamata ya yi bangarori daban daban na kungiyar APEC su sa kaimi ga yin kirkire-kirkire, da fadada bude kofa ga kasashen waje, da samun bunkasuwa tare, da raya dangantakar abokantaka dake tsakaninsu, ta haka za a sa kaimi ga samun sabon ci gaba da wadata a duniya baki daya.

A cikin jawabinsa, Xi Jinping ya yi nuni da cewa, kamata ya yi bangarori daban daban na kungiyar APEC su duba yanayin da ake ciki da aiwatar da ayyuka yadda ya kamata, ta haka za a jagoranci samun sabon ci gaba da wadata a duniya.

Na farko, ya kamata a sa kaimi ga yin kirkire-kirkire, ta haka za a samu bunkasuwa cikin sauri.

Na biyu, a fadada bude kofa ga kasashen waje, da samar da yanayi don samun ci gaba.

Na uku, a aiwatar da ayyukan sa kaimi ga samun bunkasuwa ba tare da yin la'akari da bambance-bambance ba, ta haka jama'a za su kara jin dadin rayuwa.

Na hudu, a zurfafa dangantakar abokantaka don samun moriyar juna.

Xi Jinping ya yi nuni da cewa, tabbas ne kasar Sin mai karfin samun bunkasuwa, da kara amfanawa al'ummarta, da kara yin mu'amala da sauran kasashen duniya za ta kara samar da dama da gudummawa ga nahiyar Asiya da yankin tekun Pasifik har ma ga duniya baki daya. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China