in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya gana da shugabannin kasashen Japan, Koriya ta Kudu, Chile da Philippines
2017-11-12 13:24:07 cri
A jiya Asabar a birnin Da Nang na kasar Vietnam, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da firaministan kasar Japan Shinzo Abe. A yayin ganawar, Xi Jinping ya yi nuni da cewa, Sin da Japan makwabtakan kasashe ne, kana manyan kasashen tattalin arziki na Asiya da na duniya ne. Bunkasuwar dangantakar dake tsakanin Sin da Japan ta dace da moriyar kasashen biyu, kana ya yi matukar tasiri ga yankin har ma ga duniya baki daya.

A nasa bangaren, Shinzo Abe ya bayyana cewa, Japan tana son yin kokari tare da kasar Sin, kana shekara mai zuwa ne ake cika shekaru 40 da kulla yarjejeniyar tabbatar da zaman lafiya tsakanin Japan da Sin, da kuma sa kaimi ga inganta dangantakar samun moriyar juna bisa manyan tsare-tsare.

A wannan rana kuma, shugaba Xi Jinping ya gana da shugaban kasar Koriya ta Kudu Moon Jae-in, inda ya jaddada matsayin Sin kan batun THAAD, ya ce, ya kamata bangarorin biyu su dauki alhakinsu ga tarihi da dangantakar dake tsakanin kasashen biyu da kuma jama'arsu, da tsai da kuduri mai dacewa.

A nasa bangaren, Moon Jae-in yana fatan kasashen biyu za su yi kokari tare don mayar da yin mu'amala a tsakanin manyan shugabannin kasashen biyu da hadin gwiwar kasashen biyu a dukkan fannoni. Kasarsa ta Koriya ta Kudu ta nuna goyon baya da halartar shawarar "ziri daya da hanya daya".

Kana shugaba Xi Jinping ya halarci bikin daddale yarjejeniyar yin ciniki cikin 'yanci a tsakanin Sin da Chile tare da shugabar kasar Chile Verónica Michelle Bachelet Jeria. Kana ya gana da shugaban kasar Philippines Rodrigo Duterte a wannan rana. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China