Ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa, inda aka bayyana cewa, ana bukatar mahalarta taron da aka gayyata za su hallara a ranar 9 watan Yulin domin tattaunawar a washe gari wato 10 ga watan.
De Mistura ya kara da cewa ya sake amincewa da kiran zagaye na gaba na tattaunawar a watannin Augusta da Satumba, kuma kamar yadda aka saba gudanarwa a sauran zagayen tarukan na lokutan baya, za'a gabatar da takardun gayyata ne bisa ga doka ta 2254 da MDD ta tanada.
Sanarwar ta kara da cewa, baya ga tattaunawar da za'a gudanar da bangarorin kasar ta Syria a hukumance, za kuma a gudanar da taron tuntuba da kwararru domin tsara daftarin dokoki da batutuwan shari'a a zagayen karshe na tattaunawar da aka gudanar, domin bada damar ci gaba da tattaunawar zaman lafiyar don rikicin na Syria. (Ahamd Fagam)