Abdarrahman Al-Kilani, kwamandan rundunar sojin Libya mai suna Subul Assalam mai alaka da dakarun soji dake gabashin kasar, yace bataliyar sojin ta kakkabe yunkurin fasa-kwaurin makamai da alburusai ne wanda aka yi niyyar shigar da su Sudan bayan da mazauna birnin kudancin Kufra suka yi korafin cewa wasu 'yan tada kayar baya na kasar Sudan sun kulla wata yarjejeniyar cinikin makamai da alburusai da suke son shigowa da su cikin kasar.
Al-Kilani ya ce, tuni bataliyar sojin ta tura dakarunta don yin barin wuta a wani waje mai nisan kilomita 300 dake birnin kudancin kasar, kuma sun yi nasarar cafke tsagerun tare kuma da kwace dukkan makaman da kuma alburusan.
A watan Yuni ne bataliyar Subul Assalam ta amsa kiran da babban kwamandan rundunar dake gabashi janar Khalifa Haftar ya yi, inda ya bukaci a rufe kan iyakokin kasashen Libya da Chadi da Sudan, kuma ya bada umarnin a kama duk wata mota dake zirga-zirga a tsakanin iyakokin kasar.(Ahmad Fagam)