A wani sakon da ya fitar ta shafukan sada zumunta na zamani,"UNSMIL, ta nemi a gaggauta binciko wadanda keda hannu wajen aikata kisan don gurfanar dasu a gaba shari'a.
UNSMIL ta yi Allah wadai da babbar murya game da aikata wannan mummunan laifi na kisan mutane 36 wadan da aka tsinci gawarwakinsu a yankin Abyar.
Rundunar soji dake da sansaninta a gabashin kasar ce ta bada umarni a ranar Asabar, inda ta nemi a gaggauta bincike game da faruwar lamarin.
Wata majiya daga sojoji ta bayyana cewa, mazauna garin Abyar, wanda keda tazarar kilomita 50 a kudu maso yammacin Benghazi, sun bada rahoton cewa an gano gawarwakin mutanen 36 da aka hallaka wadanda aka ga raunukan harbin bindiga a jikinsu a wani lungu a yankin.
A watan Yulin shekarar 2016 ma, jami'an tsaro sun tsinci gawarwakin wasu mutanen 14 da daure da ankwa a hannayensu a kusa da helkwatar Benghazi.
A watan Oktoban 2016, an tsinci gawarwakin mutane 10 wadanda aka hallaka su da harbin bindiga a gidan yarin soji na Benghazi.