A jiya Talata ne, jakadan kasar Sin dake kasar Afirka ta Kudu Lin Songtian da uwargidansa suka shirya wata liyafa domin murnar cika shekaru 68 da kafa jamhuriyar jama'ar kasar Sin. Ministan ayyuka da wasu wakilan gwamnatin kasar Afirka ta Kudu na daga cikin wadanda suka halarci wannan liyafa.
A jawabinsa Lin Songtian ya bayyana cewa, kasar Sin da kasashen Afirka suna da moriya iri daya, haka kuma, sassan biyu sun cimma nasarori da dama karkashin hadin gwiwar dake tsakaninsu, a halin yanzu kuma, ana fuskantar wata babbar dama ta kara bunkasa wannan hadin gwiwa.
Ya ce, a matsayinsa na sabon jakadan kasar Sin a kasar Afirka ta Kudu, yana fatan kara yin hadin gwiwa da takwarorinsa a kasar Afirka ta Kudu domin aiwatar da ra'ayoyin da shugbannin kasashen biyu suka cimma yadda ya kamata, ta yadda za a cimma sakamako masu gamsarwa.
A nasa bangare, ministan ayyuka na kasar Afirka ta Kudu Nkosinathi Nhleko ya mika sakon fatan alheri a madadin gwamnati da jama'ar kasar Afirka ta Kudu ga daukacin Sinawa yayin da suke bikin cika shekaru 68 da kafa jamhuriyar jama'ar kasar Sin. Ya kuma yaba wa kasar Sin bisa taimako da gudummawa da take bayar ga kokarin raya kasashen Afirka da kuma kiyaye zaman lafiyar duniya, yana mai cewa, an cimma nasarori da dama sakamakon hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasar Afirka ta Kudu, bisa tsarin hadin gwiwar dake tsakanin Sin da kasashen Afirka da kuma tsarin BRICS da dai sauransu. Haka kuma, ana fatan ci gaba da inganta hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu, ta yadda za a daga matsayin huldar abokantaka dake tsakanin kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare zuwa wani sabon matsayi. (Maryam)