in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jakadar kasar Afirka ta Kudu ta ce tsarin BRICS ya amfanawa kasashe masu tasowa
2017-09-01 14:03:32 cri
Yanzu haka ana dab da bude taron shugabannin kasashen kungiyar BRICS a ranar 3 ga watan da muke ciki, a birnin Xia'men dake kudancin kasar Sin. Yayin da ake shirin bude taron ne, jakadar Afirka ta Kudu a kasar Sin, Madam Dolana Msimang, ta shaidawa kafofin watsa labaru na kasar Sin cewa, tsarin kungiyar BRICS ya riga ya fara taka muhimmiyar rawa ta fuskar harkokin kasa da kasa, tare da samar da damammaki na samun ci gaba ga kasar Afirka ta Kudu da sauran kasashen dake kan hanyar tasowa. A cewarta, tsarin BRICS na da makoma mai haske, la'akari da yadda kungiyar take wakiltar moriyar kasashe masu tasowa.(Bello Wang)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China