Taron wanda zai gudana daga ranar 29 ga watan Oktoba zuwa 4 ga watan Nuwamban wannan shekara, zai kuma taimaka wajen magance matsalar talauci da jahilci ko rashin karatu da rubutu a wuraren da ake samun karuwar yawan al'umma.
Babban jami'in kididdiga a hukumar kididdigar kasar Pali Lehohla, ya ce taron zai kuma kara samar da damammaki ga zuriyar da ke tafe a fannonin da ake da matsala a halin yanzu, da yiwa gwamnati jagora kan yadda za ta sake bibiyar manufofinta na yawan al'umma.
Kimanin masana 2,000 a wannan fanni da masu tsara manufofi, kungiyoyin fararen hula da shugabannin gwamnati daga kasasahe 131 ne ake saran za su tattauna game da matsalar talauci a duniya, da mutuwar mata masu juna biyu,shekarun rayuwa a duniya. Sauran sun hada da cutar kanjamau, hanyoyin samun Ilimi da matsalar rashin ayyukan yi,da Ilimin jima'i da lafiyar kwakwalwa, da kalubalen da irin wadannan manufofi suke fuskanta a nahiyar Afirka da batun kaurar jama'a da sauran batutuwa da suka shafi yawan al'umma da na raya kasa.(Ibrahim)