in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi ya taya kungiyar INBAR murna cika shekaru 20 da kafuwa
2017-11-07 10:03:22 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sakon taya murna ga kungiyar sarrafa gora da iccen katako INBAR, dake bikin cikarta shekaru 20 da kafuwa.

Cikin wasikar tasa, Shugaba Xi Jinping ya ce cikin shekaru 20 da suka gabata, kungiyar INBAR ta taka muhimmiyar rawa wajen sarrafa gora da iccen katako a duniya, inda ta rage talauci a yankunan dake samar da su da inganta kasuwancinsu da kuma samar da dawwamamen ci gaba.

Da yake jadadda manufofin ci gaba da ake son cimmawa wadanda aka fitar yayin taron JKS na 19, shugaban ya ce kasar Sin na da nufin ci gaba da ganin dorewar zaman rayuwa tsakanin bil adama da sauran halittu, yayin da take kokarin raya muhallin hallitu da rage gurbata muhalli.

Ya ce kasar Sin za ta ci gaba da mara baya ga ayyukan INBAR, kuma a shirye kasar take ta hada hannu da kasashen waje, wajen aiwatar da muradun ci gaba masu dorewa na MDD da ake son cimmawa zuwa shekarar 2030, domin bada gudummawa wajen rayawa da zamanantar da muhallin hallitu da al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil adama. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China