in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin zai halarci taron shugabannin APEC karo na 25
2017-11-03 20:25:30 cri

Yau Jumma'a ne ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta kira taron manema labaru, inda wasu jami'ai suka yi bayani kan yadda shugaba Xi Jinping na kasar Sin zai halarci kwarya-kwaryar taron shugabannin kungiyar APEC karo na 25 a birnin Da Nang na kasar Vietnam tare da kai ziyarar aiki kasashen Vietnam da Laos.

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Li Baodong ya ce, shugaba Xi Jinping zai halarci kwarya-kwaryar taron shugabannin kungiyar APEC karo na 25 daga ranar 10 zuwa 11 ga wata, wannan shi ne karo na farko da shugaban kasar Sin zai halarci taron kasa da kasa bayan kammala babban taron wakilan JKS karo na 10, lamarin da yake da muhimmanci sosai, kuma ya jawo hankalin kasa da kasa. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China