in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping zai halarci kwarya-kwaryar taron shugabannin kungiyar APEC karo na 25
2017-11-03 10:53:28 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang, ya sanar a yau ranar 3 ga wata cewa, bisa gayyatar da shugaban kasar Vietnam Tran Dai Quang ya yi masa, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai tashi zuwa birnin Da Nang dake kasar Vietnam don halartar kwarya-kwaryar taron shugabannin kungiyar APEC karo na 25 tun daga ranar 10 zuwa 11 ga wannan wata.

Bisa gayyatar da babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Vietnam Nguyen Phu Trọng, shugaban kasar Vietnam Tran Dai Quang, babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar LPRP kuma shugaban kasar Laos Bounngang Vorachith ya yi masa, babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin kuma shugaban kasar Sin Xi Jinping zai kai ziyara a kasar Vietnam da ta Laos tun daga ranar 12 zuwa 14 ga wannan wata. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China