in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin Sin da Amurka sun yi niyyar kara kyautata huldar dake tsakanin kasashen 2
2017-11-09 16:46:24 cri
Yayin ganawar da aka yi tsakanin shugaba Xi Jinping na kasar Sin da takwaransa na kasar Amurka Donald Trump, a yau Alhamis, a birnin Beijing na kasar Sin, shugabannin 2 sun saurari rahotannin da aka gabatar dangane da musayar ra'ayin da ake yi tsakanin kasashen 2, ta fuskokin tattalin arziki da cinikayya, da aikin soja, da shari'a, da musayar al'adu, da dai sauransu, inda suka bayyana niyyarsu ta kara kyautata huldar dake tsakanin kasashen 2.

Bayan ganawa,shugabannin 2 sun gane ma idanunsu yadda aka sanya hannu kan wasu kwantiragi da yarjeniyoyin hadin gwiwa da yawan darajar kudinsu suka zarce dalar Amurka biliyan 250, wadanda suka shafi fannonin makamashi, aikin samar da kaya, da aikin gona, da zirga-zirgar jiragen sama, da aikin samar da kayayyakin lantarki da motoci, da dai makamantansu.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China