in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Najeriya ya ziyarci dakarun sojin kasar a yankin da Boko Haram ta yi kamari
2017-10-02 12:59:53 cri
A jiya Lahadi shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kai ziyarar aiki a birnin Maiduguri dake arewa maso gabashin kasar domin gudanar da bikin murnar samun 'yancin kan kasar tare da dakarun kasar dake yaki da kungiyar 'yan ta'adda ta Boko Haram a yankin.

Shugaba Buhari ya shedawa dakarun Najeriyar dake jahar Borno, dasu kasance masu nuna biyayya ga kasarsu a gaban 'yan tada kayar baya da ake samu a sassa daban daban na kasar.

Yace yin biyayya shi ne kashin bayan samun duk wata nasarar wanzar da zaman lafiya da hadin kan kasa.

Buhari yayi watsi da bukatar masu neman tada zaune tsaye a kasar, yana mai cewa yana da cikakkiyar masaniya game da abin da ya wakana a lokacin yakin basasar kasar da aka shafe watanni 30 ana gwabazawa tsakanin shekarar 1967-1970.

Yace ya halarci yakin na tsawon watanni 30. Kuma ya san abubuwa masu yawa game da kasar. Yace masu neman wargaza zaman lafiyar Najeriyar ba'a haife su ba a lokacin da kasar ta shiga cikin yakin basasar, ba su kuma fahimci mene ne kishin kasa ba.

Shugaba Buhari ya ce, gwamnatinsa zata tanadi dukkan abubuwan da ake bukata domin tallafawa dakarun tsaron kasar don gudanar da ayyukansu.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China