in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban Taron CPC ya jawo hankalin 'yan jaridar Nijeriya
2017-10-21 12:37:45 cri
Shugaban kungiyar 'yan jaridun Nijeriya Abdulwaheed Odusile, ya ce ayarin 'yan jarida biyu daga gidajen talabiji da wasu ayarin biyu na gidajen jaridun kasar ne suka zo birnin Beijing domin daukar rahoton babban taron wakilan Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin(CPC) karo na 19.

Abdulwaheed Odusile, ya ce Kasashen Nijeriya da Sin na kara zama abokan hulda na kut-da-kut, kuma kasar Sin ta taimaka sosai wajen aikin gine-gine a kasar, a don haka, ya ce ya kamata su zo daukar rahoton wannan muhimmin taro.

Ya ce 'yan jaridar kasashen yamma na bada labarai barkatai akan kasar Sin, amma su a nasu bangare, su na son rubuta na su labarin ta hanyar halartar taron da kansu. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China