in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanonin Sin dake kasashen Afirka sun ba da babbar gudummawa ga al'ummominsu
2017-10-30 13:31:12 cri

Kwanan baya, tsohon gwamnan jihar Abia ta kasar Nijeriya Orji Uzor Kalu ya bayyana a nan birnin Beijing cewa, kamfanonin kasar Sin dake kasashen Afirka sun ba da gudummawa ga al'ummomin kasashensu.

Bisa gayyatar da jami'ar nazarin harkokin kasuwanci da kasashen waje da ke birnin Beijing UIBE dake kasar Sin ta yi masa, Dr. Uzor Kalu ya kai ziyara a jami'ar, inda ya ba da jawabi mai taken "fadada hanyoyin tattalin arziki, da rawar da kamfanoni masu zaman kansu da gwamnati zasu taka".

Kuma a yayin da yake zantawa da wakilan sashenmu, ya bayyana cewa, a halin yanzu, akwai kamfanonin kasar Sin da dama a kasarsa, har ma a duk fadin kasashen Afirka, wadanda suke samun karbuwa sosai a kasashen, sabo da babbar gudummawar da suka baiwa jama'ar kasashen, musamman ma a fannonin gina ababen more rayuwa da kuma harkokin sadarwa.

Bugu da kari, ya ce, akwai babbar dama a kasuwannin kasar Nijeriya, kuma tana sa ran karfafa hadin gwiwar dake tsakaninta da kamfanoni na kasar Sin, domin koyon fasahohin zamani daga wajen kasar Sin ta fuskar ayyukan noma da kimiyya da fasaha da dai sauransu, ta yadda za a bada karin gudummawa ga al'ummomin kasashen biyu baki daya. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China