A yayin wani taron manema labaru da ya gudana a jiya, a ofishin jakadancin kasar Saudiyya dake Burtaniya, Adel al-Jubeir ya ce, bangarorin Saudiyya da Iran, ba su yi wata mu'amala da ta shafi siyasa ba in ban da harkar ibada ta aikin hajji.
Don haka ya zuwa wannan lokaci ba batun kome ga dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. Adel al-Jubeir ya kara da cewa, idan kasar Iran tana son kyautata dangantakar dake tsakaninta da Saudiyya, to ya zama wajibi ta yi gyaran fuska ga manufofinta na diflomasiyya, ta kuma dakatar da nuna goyon baya ga ta'addanci, kana ta daina tsoma baki kan harkokin cikin gidan sauran kasashe, ta kuma rika girmama dokokin kasa da kasa. (Sanusi Chen)