Wannan doka da sarki Salman ya bayar na zuwa ne bayan shiga tsakanin da Sheikh Abdullah bin Ali bin Abdullah bin Jassem Al Thani na Qatar ya yi.
Yarima Mohammed bin Salman na Saudiya ya gana da basaraken na Qatar, wanda ya tabbatar da hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu, inda ya bukaci mahukuntan na Saudiya da su budewa alhazan kasar Qatar din kan iyakar Salwa.
Haka kuma Sarki Salman ya umarci jiragen sama na kasar Saudiya da su kwashe dukkan alhazan kasar ta Qatar, ya kuma alkawarin zai biya kudaden jigilar tasu a cikin aljihunsa.
A watan Yunin wannan shekara ce dai kasar Saudiya ta jagoranci kasashen hadaddiyar daular Larabawa, da Bahrain, da Masar, domin katse huldar diflomasiya da na kasuwanci da kasar Qatar, saboda zargin kasar Qatar da tsoma baki a harkokin cikin gidansu da kuma taimakawa ayyukan ta'addanci, zargin da Qatar din ta musanta.
A sakamakon wannan takun saka ne, kasar Saudiyar ta rufe kan iyakarta da Qatar sannan ta haramtawa jiragen saman kasar Qatar din ratsawa ta sararin samaniyarta. (Ibrahim Yaya)