Cikin wata sanarwa da Alaa Youssef mai Magana da yawun kamfanin dillancin labaran gabas ta tsakiya (MENA) ya rawaito, ya bayyana cewa, al- Sisi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da Mohamed Fayek, shugaban hukumar kare hakkin dan adam ta kasar Masar.
Fayek ya gabatar wa al- Sisi rahoton hukumar kare hakkin dam adam ta shekarar 2016-2017 ne, wanda ya yi cikakken bayani game da manyan kalubaloli da suka shafi batun kare 'yancin dan adam da kuma irin matakan da za'a bi wajen magance su.
Shugaban na Masar yayi alkawarin zai nazarci rahoton hukumar, kana zai amince da irin shawarwarin da rahoton ya gabatar.
Fayek, yayi amanna cewa, kokarin da kasar Masar ke yi na yaki da ta'addanci tare kuma da kare tsaron kasar, hanya ce da zata tabbatar da samun dauwamamman zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar.(Ahmad Fagam)