Ghassan Salame ya bayyana haka ne lokacin da yake ganawa da manema labarai jiya Talata, bayan ya gana da ministan harkokin wajen kasar Mohammed Sayala a Tripoli, babban birnin Libya.
A ranar Asabar da ta gabata ne aka kammala zagaye na biyu, na tattauna yarjejeniyar yi wa tsarin siyasar kasar garambawul a kasar Tunisiya, wanda shirin wanzar da zaman lafiya na MDD dake Libyan ya dauki nauyi.
A tsakiyar watan Satumba ne Ghassan Salame, ya gabatar da wani kuduri dake da nufin kawo karshen rikicin siyasa a kasar. Kudurin ya kunshi yi wa yarjejeniyar ta yanzu da MDD ke marawa baya garambawul da gudanar da babban taron kasa karkashin jagorancin MDD, wanda dukkan bangarorin siyasar kasar za su halarta da kuma zaben shugaban kasa da mambobin majalisar dokoki. (Fa'iza Mustapha)