in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Amurka ya fara ziyarar aiki a Sin
2017-11-08 14:57:39 cri

Shugaban Amurka Donald Trump ya iso birnin Beijing na kasar Sin yau da yamma, bisa gayyatar da shugaban kasar Xi Jinping ya yi masa.

Wannan shi ne karo na farko da shugaba Trump ya kawo ziyarar aiki a Sin bayan da ya zama shugaban Amurka, kuma bako na farko da kasar ta samu bayan kammala babban taron wakilan JKS ta kasar karo na 19.

A yayin ziyararsa a kasar Sin, shugabannin kasashen biyu za su tattauna kan manyan batutuwan dake jan hankulansu, domin raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu cikin sabon zamani. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China