in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Amurka Donald Trump zai kawo ziyara kasar Sin
2017-11-02 09:50:01 cri
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, Lu Kang ya ce, bisa goron gayyatar da shugaba Xi Jinping ya ba shi, shugaban Amurka Donald Trump zai kawo ziyarar aiki kasar Sin daga ranar 8 zuwa 10 ga watan nan da muke ciki. A yayin ziyarar, shugabannin biyu za su yi musayar ra'ayi kan alakar kasashen biyu gami da wasu muhimman batutuwan kasa da kasa da na shiyya-shiyya.

Lu Kang ya ce, kasar Sin na fatan yin kokari tare da Amurka, domin tabbatar da samun nasarori a yayin ziyarar Trump a kasar Sin gami da ganawarsa da Xi Jinping, da kuma sanya sabon kuzari wajen habaka dangantakar kasashen biyu.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China