in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin Sin da Amurka ta haifar da moriyar juna
2017-11-08 11:04:50 cri

A yau ne shugaba Donald Trump zai fara wata ziyarar aiki ta kwanaki uku a nan kasar Sin, ziyara ta farko da shugaban zai kawo kasar ta Sin tun bayan kammala babban taron wakilan JKS karo na 19.

Sai dai tun kafin ganawar shugabannin kasashen biyu a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, batun hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin Sin da Amurka ya sake janyo hankulan kasashen duniya.

Sai dai duk da takaddamar dake tsakanin su, an samu karuwar hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya cikin sauri tsakanin kasashen biyu, baya ga karin moriya da al'ummomin kasashen biyu suka samu.

Ana kuma sa ran ganawa tsakanin shugabannin kasashen biyu, za ta bunkasa musaya tsakanin kasashen biyu mafiya karfin tattalin arziki a duniya.

Haka kuma yayin da manyan kasashen ke kokarin daidaita tattalin arzikinsu, harkokin cinikayya tsakanin sassan biyu ta kara inganta. A shekaru goman da suka gabata, kayayyakin da Amurka take fitarwa zuwa Sin ya karu da kaso 11 cikin 100 a shekara, yayin da kayayyakin da Sin take fitarwa zuwa Amurka ya karu da kaso 6.6 ne kawai cikin 100.

Ko da yake har yanzu kasar Sin tana samun rara a cinikayyar da take yi da Amurka, amma haka ba ya nufin kasar ta Sin tana amfana fiye da Amurkar. Kimanin kaso 40 cikin 100 na rarar cinikayyar na shiga aljihun kamfanonin Amurka ne dake kasar Sin.

Bayanai na nuna cewa, cinikayya tsakanin Amurka da kasar Sin ya taimakawa iyalan Amurka suna iya adana dala 850 ko wace shekara. A shekarar 2015, harkokin cinikayya da zuba jari tsakanin sassan biyu ta samar da guraben ayyukan yi miliyan 2.6 a kasar ta Amurka. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China