in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Amurka sun cimma nasarar bincike wani laifin keta ikon mallakar ilmi cikin hadin gwiwa
2017-11-08 14:01:07 cri
Ma'aikatar tsaron jama'a ta kasar Sin da ma'aikatar tsaron kasar Amurka sun yi nasarar binciken wani laifin keta 'yancin mallakar fasaha, inda suka kama masu aikata laifi 36, wadanda suka yi wasu kayayyakin jabu, yayin da suke kokarin sayar da su a wasu sassan kasashen duniya

Haka kuma, a lokacin da aka lalata sansanoninsu 7, an samu hajojin da suka hada da jakakkuna masu tambarin "LOUIS VUITTON" da agogo da dai sauransu sama da guda dubu 3, wadanda aka yi kisayin cewa, darajar kudinsu ya kai RMB miliyan dari 1.

A halin yanzu kuma, hukumomin shari'a suna gudanar da bincike kan wasu shafunan intanet dake sayar da kayayyakin jabu, da ma wadanda ke sayan irin wadannan kayayyaki. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China