in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen Sin da Amurka sun gudanar da tattaunawar farko game da dokoki da tsaron yanar gizo
2017-10-05 17:20:04 cri
A jiya Laraba ne kasashen Sin da Amurka suka yi tattaunawa irinta ta farko a kan batutuwan da suka shafi martaba dokoki da tsaron yanar gizo, inda sassan biyu suka cimma matsaya kan batutuwan da suka shafi yaki da ayyukan ta'addanci, da safarar miyagun kwayoyi da tsaron yanar gizo da batun kaurar jama'a.

Mamba a majalisar gudanarwar kasar Sin Guo Shengkun da ministan tsaron jama'a, Atoni janar na Amurka Jeff Sessions da mai rikon mukamin sakataren tsaron cikin gida na Amurka Elainbe ne suka jagoranci taron.

A yayin ganawar Guo ya yi kira ga sassan biyu da su mayar da hankali kan hadin gwiwa kana su yi kokarin warware bambance-bambancen dake tsakaninsu, kara yin hadin gwiwa a fannin dokoki da tsaron yanar gizo a matsayin sabbin fannonin hadin gwiwar kasashen biyu, da kara kokari wajen tabbatar shugabanci mai nagarta a duniya da samar da yanayi da makoma mai kyau ga bil-adama.

A nata bangaren kasar Amurka, ta jaddada muhimmancin hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu a fannin da ya shafi dokoki da tsaron yanar gizo, duba da yadda sassan biyu ke fuskantar barazana iri guda da kuma muradun da suke da shi a wadannan fannoni.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China