in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Amurka na shirye-shirye game da ziyarar da Trump zai kawo Sin
2017-10-13 20:05:09 cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, Madan Hua Chunying ta shaidawa taron maname labarai a Jumma'ar nan cewa, kasashen Sin da Amurka suna kimtsawa don tabbatar da cewa, ziyarar da shugaba Trump na Amurkar zai kawo kasar Sin a wata mai zuwa, ta haifar da kyakkayawan sakamako.

Madan Hua ta ce ko da a jiya Alhamis, sai da mamba a majalisar gudanarwar kasar Sin Yang Jiechi ya tattauna da sakataren harkokin wajen kasar Amurka Rex Tillerson inda suka yi musayar ra'ayoyi game da dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, kana suka bayyana kudurinsu na ci gaba da aiki tare game da shirye-shiryen wannan ziyara, don tabbatar da cewa, ziyarar ta haifar da da mai ido.(Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China