in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta bayyana rashin jin dadinta kan yadda jirgin ruwan yakin Amurka ya ratsa yankin ruwanta ba tare da izni ba
2017-10-11 20:14:14 cri

Kasar Sin ta bayyana rashin jin dadinta kan yadda jirgin ruwan yakin Amurka ya kutsa cikin yankin tekun kudancin kasar ta Sin a jiya Talata.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying wadda ta bayyana hakan yau yayin taron manema labarai, ta ce a jiya ne jirgin ruwan yakin na Amurka mai suna Chafee ya shiga tsibiran Xisha dake tekun kudancin kasar Sin, inda ya fake da sunan 'yancin yin zirga-zirga ya kuma gudanar da wasu ayyuka ba tare da samun izni daga mahukuntan kasar ta Sin ba.

Madam Hua ta ce, abin da jirgin ruwan sojan na Amurka ya gudanar ya saba wa dokokin kasar Sin da na kasa da kasa, kana ya keta 'yanci da muradun kasar Sin, baya ga yadda ya sanya rayukan mazauna yankin a cikin hadari.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China