in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An fara yin amfani da Alipay a kamfanoni dubu 10 na kasar Afirka ta Kudu
2017-08-31 13:18:07 cri
Kamfanin Ant na kasar Sin ya sanar a jiya cewa, an fara yin amfani da hanyar biyan kudi ta tsarin Alipay a kamfanoni dubu 10 na kasar Afirka ta Kudu, tsarin da zai baiwa Sinawa masu yin amfani damar biyan kudi ta Alipay yayin da suke yawon shakatawa a kasar Afirka ta Kudu.

Rahotanni na cewa, kamfanonin kasar Afirka ta Kudu da kamfanin Zapper ne suka shigo da hidimar Alipay cikin kasar Afirka ta Kudu. A matsayin abokin hadin gwiwa na farko na Alipay, kamfanin Zapper ya samar da hidima a fannonin otel, sayar da kayayyaki, tikiti, ciniki ta intanet, bada kayayyaki kyauta, ajiye mota, biyan kudin makamashi da sauransu.

A ranar 27 ga watan Yuni ne, aka fara yin amfani da tsarin na Alipay karo na farko a kasar Afirka ta Kudu, inda aka yi amfani da tsarin wajen biyan tikitin bas na yawon shakatawa a kasar.

A halin yanzu, ana amfani da tsarin Alipay a kamfanoni fiye da dubu 200 a kasashe da yankuna 30 ciki har da kasashen Turai, da Amurka, da Japan, Koriya ta Kudu, kasashen yankin kudu maso gabashin Asiya, yankin Hongkong, yankin Macau, yankin Taiwan da sauransu, a fannonin da suka shafi abinci, kantuna yau da kullum, kantin sayar da kayayyaki da ba a biyan haraji, wuraren yawon shakatawa, filayen jiragen sama da sauransu. (Zainab Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China