Hukumomi a kasar Kenyan sun tsaurara tsaro a muhimmin garin Lamu dake bakin teku gabanin fara bukukuwan kasar wanda ake sa ran farawa a gobe Alhamis.
Baki mahalarta bikin gargajiya na Lamu, wanda za'a gudanar da shi har zuwa ranar Lahadi mai zuwa, sun isa garin tun a ranar Talata, sun tabbatar da tsaurara tsaro a yankunan.
Jami'i mai kula da yankin Nelson Marwa, ya ce, jami'an 'yan sanda na ci gaba da gudanar da sintiri a wuraren da za'a gudanar da bukukuwan wadanda suka hada da hawan dawakai, da gasar yin ninkaya, da zane zane, da dafa abinci, da kuma rubuta wakoki.
Ya ce, aikin sintiri da ake gudanarwa a yankin Boni, ya taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da tsaro a muhimmin garin, wanda a shekarun baya ya sha fama da hare haren ta'addanci daga mayakan Al-Shabaab.
Yan bindiga sun taba kaddamar da hare hare a garin a shekarar 2014, inda suka hallaka mutane sama da 100, lamarin da ya haddasa koma baya wajen karuwa masu yawon bude ido zuwa yankin.(Ahmad Fagam)