in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta zuba yuan biliyan 2000 a fannin yawon shakatawa a shekarar 2020
2016-12-14 20:29:26 cri

A yau Laraba ne hukumar raya kasa da yin gyare-gyare ta kasar Sin tare da hadin gwiwar hukumar harkokin yawon shakatawa ta kasar suka kaddamar da takardar aiwatar da manyan ayyukan yawon shakatawa da nishadantarwa. Bayanai na nuna cewa, harkokin yawon shakatawa sun kara taimakawa wajen raya tattalin arzikin kasar Sin. Matsakaicin yawan kudin da aka zuba a fannin yawon shakatawa kai tsaye a nan kasar Sin ya karu da kashi 20 cikin dari a kowace shekara, kana ya zuwa shekarar 2020, jimillar kudin da za a zuba a fannin yawon shakatawa za ta kai kudin Sin yuan biliyan dubu 2 baki daya. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China