in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kenya da Uganda da Rwanda na kokarin raya sha'anin yawon shakatawa a gabashin Afirka
2017-03-02 15:48:11 cri
Kwanakin baya ne, kasashe uku dake gabashin Afirka da suka hada da Kenya, da Uganda gami da Rwanda, suka kaddamar da wani aiki ta yanar gizo ta Intanet, game da raya wata kasuwar yawon shakatawa ta bai daya a gabashin Afirka, a kokarin kara jawo hankalin masu sha'awar yawon bude ido zuwa wannan yanki.

Alkaluman kididdiga na nuna cewa, a shekarar 2015, adadin mutanen da suka ziyarci Kenya ya kai miliyan 1.2, kana yawan mutanen da suka je Uganda ya kai miliyan 1.1, yayin da mutanen da suke je yawon shakatawa kasar Rwanda ya kai miliyan 1.3.

A wani labarin kuma, wani rahoton da bankin raya Afirka ya fitar, a shekara ta 2014, ya nuna cewa, sama da mutane miliyan 65 ne suka ziyarci nahiyar Afirka don yawon shakatawa, adadin da ya kai kashi 5.8 bisa dari na jimillar yawan mutanen da suka je yawon shakatawa a fadin duniya.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China