in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sudan ta bukaci kasashen Larabawa da su kai zuciya nesa
2017-06-06 10:01:10 cri
Kasar Sudan ta bayyana rashin jin dadinta game da shawarar da wasu kasashen Larabawa suka yanke ta katse huldar diflomasiya da kasar Qatar.

Wata sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Sudan din ta fitar, ta ce, ba ta ji dadin wannan lamari da ya faru ba, tana mai cewa matakin ya sosa ran al'ummar Sudan da ma daukacin kasashen Larabawa.

Sanarwar ta kara da cewa, bisa la'akari da hakkin da ya rataya a kanta ta fuskar addini da jini da kuma tarihin dake tsakaninsu, Sudan tana kira da a kai zuciya nesa kana a zauna a kan teburin sulhu domin warware duk wasu bambance-bambance ta hanyar amfani da hikima da sanin ya kamata domin kare martaban muradun kasashe da ma al'ummar Larabawa baki daya.

Kasar Sudan ta sake jaddada kudurinta na yin duk mai yiwuwa wajen ganin an kwantar da wutar wannan takaddama ta yadda al'amura za su daidaita kamar yadda suke a baya. Ta yadda hakan zai dace da muradun al'ummar dake shiyyar.

A jiya ne dai kasashen Saudiya da Masar da hadaddiyar daular Larabawa, da Bahrain da Yemen da Libya da Maldives suka katse hulda da kasar Qatar, bisa zarginta da goyon bayan ayyukan ta'addanci. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China