Kamfanin dillancin labarai na KUNA ya ruwaito ministan harkokin wajen Kuwaitin cewa, kasar Qatar a shirye take ta tattauna da kasashen domin lalibo bakin zaren warware sabanin dake tsakaninsu, kuma za ta karfafa dukkan matakai da za su tabbatar da zaman lafiya da tsaro a yankin.
Sanarwar ta zone bayan da kasashen yankin Gulf din da suka hada da Saudi Arabia, Hadaddiyar daular Larabawa (UAE) da Bahrain, da kuma kasar Masar, har ma da sauran kasashen da ba na yankin Gulf din ba, suka zargi Qatar da hannu wajen taimakawa kungiyoyin 'yan ta'adda da kuma yin katsalandan cikin harkokin cikin gidan wasu kasashe.
Cikin majalisar hadin kan kasashen 6 na yankin Gulf (GCC), Kuwait da Oman ne kadai ba su bi sahun takwarorinsu ba, wajen yanke hulda da Qatar, kuma shugabannin Kuwait na ci gaba da tattunawa da bangarorin da abin ya shafa domin lalibo bakin zaren kawo karshen takaddamar. (Ahmad Fagam)