Shugaba Xi ya yi wannan furuci ne a lokacin da yake zantawa da takwaransa na Rashar Vladimir Putin ta wayar tarho.
A lokacin tattaunawar tasu, Putin ya taya shugaba Xi murnar sake zabensa a matsayin babban sakataren jami'yyar kwaminis ta kasar Sin ta CPC.
Bugu da kari, shugaba Putin ya bayyana farin cikinsa dangane da kammala babban taron jami'yyar CPC karo na 19 cikin nasara.
Da yake nuna gamsuwarsa game da taya murnar da Putin ya gabatar masa, Xi ya bayyana cewa, babban taron da aka kammala ya kunshi manyan tsare tsare na raya jami'yyar CPC da kuma kasar Sin ne, wanda ya samu amincewar magoya bayan jam'iyyar CPC kimanin mutane miliyan 89.
"Muna da kwarin gwiwa na jan ragamar al'ummar Sinawa domin cimma burin gina babbar kasa mai karfin cigaba, wanda hakan shi ne babban nauyin dake wuyan jam'iyyar CPC a bisa tarihi", inji shugaba Xi.(Ahmad Fagam)