Shugaban wanda ya yi wannan tsokaci, yayin ganawar sa da mambobin hukumar bada shawarwari na jami'ar Tsinghua a babban dakin taruwar jama'a dake nan birnin Beijing a jiya Litinin, ya ce Sin na tallafawa ci gaban tattalin arzikin duniya, wanda hakan ya zamo hanyar cimma moriya gare ta, da ma sauran kasashen duniya.
Da ya tabo batu game da taron wakilan JKS na 19 da ya kammala 'yan kwanakin baya, shugaban na Sin ya ce taron ya yi matukar armashi, ya kuma dada haskaka kwarin gwiwar da Sin ke da shi, game da aiwatar da manufofin gurguzu mai halayyar musamman ta kasar Sin.
Shugaba Xi ya kara da cewa, kasar sa za ta ci gaba da gudanar da sauye sauye a dukkanin fannoni, tare da tabbatar da tsaron kasa, da 'yancin mulkin kai, da ci gaba mai dorewa.
Ya ce basira jigo ce ta kirkire kirkire, kuma za a iya gina ta ne kadai, idan aka ilmantar da al'umma yadda ya kamata.(Saminu Alhassan)